Anyi Garkuwa Da Malamin Jami’a Da Dalibai Biyu A Jihar Kaduna



Anyi garkuwa da malami da dalibai 2 na kwalejin kiwon lafiya da ke Pambegua, Kaduna da  jiya a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.

Wannan na faruwa ne bayan anyi garkuwa da wani dan majalisan dokokin jihar Kaduna a hanyar makon da ya gabata.

Wani mazaunin Birnin Gwari yace dalibai da malaman suna tafiya ne a motar makaranta inda masu garkuwa da mutanen suka tafi dasu cikin wani daji. 

Daga baya aka kai motan makarantan ofishin yan sanda a Birnin Gwari.

Wata majiya ta ce an kashe mutum daya a hanyar gabanin lokacin yayin da suka budewa wata motar haya wuta.

Malamin da dalibansa sun nufi kai ziyara ne ga wata abokiyar aiki a Birnin Gwari.

Comments 0

Your email address will not be published.

Anyi Garkuwa Da Malamin Jami’a Da Dalibai Biyu A Jihar Kaduna

log in

reset password

Back to
log in