Ansaru ta dauki alhakin hari kan sarkin Potiskum


Kungiyar yan ta’adda ta Ansaru ta dauki alhakin kai hari kan ayarin sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram.

An kai wa sarkin hari ne akan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Audu Bulama Bukarti, lauya mai fashin baki kuma mai kare hakin dan Adam shine ya bayyana haka cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya nuna cewa harin na nufin kungiyar Ansaru da aka kafa a shekarar 2012 ta kara dawowa.

Kungiyar ta fitar da sanarwar kai harin ta kafar yada labarai ta Thabat da kungiyar Al-qaida ke amfani da ita.

Wannan hari na biyu da kungiyar ta kai tun bayan wanda ta kai a shekarar 2013 a wani gida inda wasu ma’aikata yan kasashen waje na kamfanin gine-gine na Setraco suke dake garin Azare.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like