Ana Zargin Shugabannin Jami’iyar APC A Adamawa Da Yunkurin Canza Sunayen Masu Zabe Kafin Fidda Dan Takarar Gwamna
Masu korafin sun fadi hakan ne a wurin wani taron maneman labarai da suka kira a birnin Yola babbar fadar gwamnatin jihar Adamawa domin bayyana damuwan su da kuma halin da jami’iyar ke ciki a jihar.

Mutane biyar ne suka sayi takardan neman shiga takarar kujera gwamna a jami’iyar APC a jihar Adamawa, kwatsam sai uku daga ciki suka kira taron manema labarai a kan zargin cewa ana kokarin canza sunayen masu kada kuri’a a jami’iyar ko kuma delegate a turance.

Alhaji Umar Mustafa Madawaki daya daga cikin masu neman gurbin takarar kujerar gwamnan jihar, ya bayyanawa manema labarai cewa, sun yi bincike mai zurfi a kan wannan batu kuma lallai ba zasu lamunta ba kuma an saba yarjejeniyar da aka kulla dasu a wajen taron da aka yi dasu a kan shiga zaben fidda gwanin da za a yi a ranar 20 ga watan nan na Mayu, 2022

A nashi bagaren shugaban jami’iyar APC na jihar Adamawa Alhaji Ibrahim Bilal ya ce wannan maganar jita-jita ne kawai ko kuwa shaci-fadi ne domin kuwa maganar tasu bata da tushe bare makama, sai dai a iya cewa an gudanar da komai bisa tsari da adalci.

Ya kara da cewa “bamu kammala gudanar da shirye shiryen takarar ba, saboda sai an kai takardan sunayen ‘yan masu zabe a shelkawatan jami’iya ta kasa a tabbatar da ‘yan zaben, a don haka babu inda wani zai iya sauyawa ko cire sunan wani mai kada kuri’a a daidai wannan lokacin,” in ji shi

Masana sun yi tsokaci a kan wannan batu duba da cewa wannan kartan kasa da nunawa juna yatsa ya kunno kai a yayin shirye shiryen tinkarar babban zaben mai zuwa sai kuma gashi an fara nunawa juna yatsa a jami’iyar APC na jihar Adamawa.

Dr Mahadi Abba malami ne a jami’ar Modibbo Adama dake Yola a jihar Adamawa ya ce lallai jami’iyar APC ta kula kada wannan batu ya janyo mata faduwa a bababan zaben na badi.

Ya ce jami’iyar bata gaggauta daukar mataki ba, ta kyale batun har wasu suka aikata abin da ake korafi a kai, zai janyo musu cikas a babban zaben na shekarar 2023.


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg