Ana zargin dan shekara 40 da aikata fyade kan yarinya yar shekara 8


Yan sanda a jihar Benue suna tsare da wani mutum mai shekaru 40 kan azrgin da ake masa na aikata lalata da wata yarinya yar shekara 8 a cikin garin Makurdi babban birnin jihar.

Mai magana da yawun rundunar yans sandan jihar, Catherine Anene, ta ce an kama mutumin da ake zargi ne bayan da aka kai kara ofishin yan sanda na “A” dake makurdi.

Ta ce yarinyar na tallan ruwan Pure Water inda mutumin ya yaudareta da sunan zai siya daga nan ya jata cikin dakinsa kana yayi mata fyade.

Anene ta kara da cewa ana cigaba da binciken mutumin da ake zargi yayin da ake tsare da shi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like