Ana Wata Ga Wata: Farashin Naman Kare Ya Yi Tashin Goron Zabi A Zaria


Masu iya magana sun ce, abincin wani gubar wani. Wani matashi mai sana’ar fawa amma ta kare mai suna Dadi mazaunin anguwar Tabo dake Samaru a karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna ya tabbatar wa wakilinmu cewa yanzu naman kare ya yi tashin gwauran zabo a duk fadin kasuwannin naman kare dake Zariya, don haka duk wani mai mu’a’mula da shi sai dai ya yi hakuri, karancin karnukan ne ya kawo hakan.

Dadi dan kimamin shekaru 30 ne a duniya a cewarsa ya kai a kalla shekaru 11 yana sana’ar fawa ta kare kuma da ita ya ke ci da sha har ya taimaki iyayensa da wani abu.

Dadi ya ce abin da yake burgeshi a yanzu shine, yadda naman karen ke kara daraja a yanzu, kuma a lokaci guda masu cin naman karen suna kara yawa.

Ya ce, a lokutan baya kabilu kadan ne ke cin naman kare, amma yanzu da sauran kabilun suka fahimci yadda karen yake da dadi to, yanzu rububin sa ake yi a duk fadin kasuwannin kare dake fadin kasan nan.

To, ko ta yaya mahautan karen ke samun galabar kare mai cizo idan ya zo mahautar ta kare, inda za a yanka shi? Dadi ya ce, yadda ake samun kwararru wajen kayar da bijimin sa to, haka mu ma muke da kwararru wajen zamge kare komin fadansa kuma komin girmansa.

Da aka tambaye shi ko a ina ake sayo karen ga masu bukatar cinsa? Sai mahaucin ya ce, da yawan lokaci akan kawo wasu mahautar karnuka ne, kuma yadda ake cika mota tirela da shanu daga arewa zuwa kudancin Nijeriya haka muke cika mota tirela da karnuka daga nan arewa zuwa kudancin Nijeriya.

Kuma a cewar mahaucin karen a yanzu haka da kadan farashin kilon naman sa ya zarta farashin naman kare a kasuwa nama.

Kuma hakan ya sa an samu karin masu kiwon kare don ci da masu kiwon kare don tsaro. Wanda hakan ya sa kasuwar kare ta kara daraja kuma sana’ar fawa ta karen ta kara daukaka, musamman a jihohin arewa da kudu baki daya.

Dadi ya ce, a yanzu kalubalen da sana’ar fawar kare ke fuskanta shine matsalar tsaro da ke fuskantar a kasa baki daya, saboda a lokutan baya sukan yanka kare 10 zuwa 20 kuma su kare lokaci gida saboda manyan mutane na zuwa suna siyan naman amma yanzu bai wuce su yanka 5 ba saboda an samu canjin kasuwa manya mutanen na jin tsoron zuwa sayen naman karen don satar jama’a da ake fama da shi a halin yanzu da yin garkuwa da ake fama da su.

Kalubale na biyu shine yadda gwamnati take tallafawa kungiyar mahautan shanu da kudi don karfafa sana’ar fawa to, su basa samun wannan tallafi, don haka ya yi kira ga gwamnati da su rika sanya mahautan kare a cikin tsari saboda muhimmancin su ga al’umma.

Bincike ya nuna cewa akan samu masu mu’a’mula da naman kare a kowacce kabila musamman a barikokin soja ko barikokin ‘yan sanda da akan kira Mami Market.

Wasu masu cin naman karen dai sun tabbatar da cewa naman kare yana da zaki fiye da naman akuya ko saniya bisa la’akkari da abincin da ya ke ci, kuma bincike ya nuna kare na da saurin yaduwa domin a shekara karya kan haifi yara 15 kuma bashi da wabi kamar sauran dabbobi.

Kuma biciken ya nuna cewa masu kiwonsa don tsaro sun fi masu kiwonsa don cinsa samun riba bisa dalili guda 1 na cewa zai wahala kaga wani yayi kiwon kare don ya yanka ya ci, kuma duk karen da ka ga an yankashi to, ko bai da lafiya ko an sato shi ne, don haka ya sa masu kiwon sa don tsaro sun fi masu sana’ar cin sa riba.

Halittar kare wata halitta ce mai tattare da baiwa kala kala cikinsu akwai sabo da kaifin basira da rikon amana. Kare wasu kan kiwonsa don tsaron gida wasu kuma don kiwon dabbobi wasu kuma don binciken halittun dabbobi.

Wasu suna cin namansa wasu kuma ba sa ci.

Duk da son da wasu ke yin masa amma yakan zaman abin tsoro a wasu lokutan mussamman yayin da ya kamu da ciwon hauka da in ya ciji mutum ya kan kai shi barzahu a lokaci kalilan. Ya kan kuma taka muhimmiyar rawa a wajen harkar tsaro ko isar da sako ga ubangijinsa ta hanyar yin haushi da kuma dabarar da aka koyar da shi.


Like it? Share with your friends!

-1
87 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like