Ana Shirya Manakisar Batawa Sarkin Kano SunaA yunkuri da wasu suke yi na ganin sun kirkiro da sharri daban-daban na  ganin sun kala wa Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, 

A yanzun haka sun yi wani zaman sirri inda suke kokarin fid da bayanan karya na ganin sun hada shi fada da fadar gwamnatin tarayya da duk mai sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa.

Bincike ya nuna cewa, wadannan mutane sun nemi wasu kafafen yada labarai na yanar gizo inda aka ware makudan kudi don ganin an yayata labaran karya akan cewa tsofafin shuwagabanni kasa uku wato Janar Olusegun Obasanjo, Janar Badamasi Babangida da Janar Abdulsalam Abubakar sun yi zama na musamman inda suka tsayar da Mai Martaba Sarkin Kano a kan dan takarar shugaban kasa na 2019.

Wadanda suka hada taron sirrin sun ce, sun tabbatar wannan zai jawo wa Sarkin bakin jini daga wajen magoya bayan Buhari.

Daya daga cikin ‘yan jaridu da ya halarci wannan zama, ya ce akwai shirye-shirye da dama da aka tsara don ganin an tozarta Sarkin a idon jama’a inda aka yi wa mahalarta zaman alwashin ba su kudade  da dama.

Comments 0

Your email address will not be published.

Ana Shirya Manakisar Batawa Sarkin Kano Suna

log in

reset password

Back to
log in