Ana Shan Bakar Wahala A Mulkin Buhari – Jarumar Fim Omotola Jalade


Wata fitacciyar jarumar wasan fina-finan kwaikwayo na kudancin Najeriya, Nollywood, mai suna Omotola Jalade, ta soki salon mulkin Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari, inda ta bayyana cewar ‘yan Nijeriya na shan bakar wahala a mulkinsa, sannan ta koka da asarar rayukan da ake samu a wasu sassan kasar nan.

Omotola ta bayyana hakan ne a shafinta na sada zumunta, wato Tuwita, in da ta koka a kan kashe-kashen rayukan jama’ar da basu ji ba, balle su gani ba da ‘yan taadda ke yi.

Kazalika ta bayyana kisan farar hula da jami’an tsaro ke yi a matsayin abun takaici, sannan ta kara da cewa matukar gwamnatin Buhari ba ta yi maganin wadannan matsaloli ba, za su iya haifar da wata matsalar mai girman gaske.

Omotola ta bukaci gwamnatin Buhari da ta yi wani abu cikin gagga wa a kan halin da kasar nan ke ciki, matukar da gaske gwamnati na son ci gaban kasa da jama’ar cikinta, ta ce kin daukan matakan gagga wa domin magance matsalolin da Najeriya ke ciki, ba zai haifar wa da kasa da mai ido ba

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like