AN ZARGI DPO DA KISAN BUDURWA


Hukumar yansanda a jihar Katsina ta cika hannu da wani jami’inta mai mukamin DPO mai suna; Garba talawai, sakamakon mutuwar wata budurwa mai shekaru goma sha shidda, mai suna Rabi Abdullahi.

Ita wannnan budurwa data rasu ance mai aikice a gidan Sa’adiyya Danyaya Wadda budurwace ga DPO talawai.

Jami’in Hudda da jamaa Na rundunar yan’sanda Na jihar katsin wato Gambo isah ya ambata haka yayin zantawarsa da manaima labarai a Yau asabar.

Shedun gani da ido sunce “Anga gawar Rabi Abdullah ne da misalin Karfe sha biyun Rana a cikin jeji a ranar jumaa, yayinda aka shaidawa jami’an yansanda suka garzaya da gawar asibitin dake a garin mashi Na jihar Katsina.

Bayan kai gawar asibiti malaman lafiya sunce tun ranar alhamis DPO talawai yakai gawar asibitin Na mashi, a motarsa kirar Toyota Carin.

Tuni Jamian yansanda suka tusa keyar DPO din tareda budurwarsa domin gudanar da bincike.


Like it? Share with your friends!

-1
46 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like