An zabi, Kwamared Ahmad Labbo a matsayin sabon shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa NULGE, kwanaki kadan bayan mutuwar Ibrahim Khalil wanda ya ke shugabantar kungiyar har zuwa lokacin da ya rasu.

Labbo ya zamo sabon shugaban kungiyar ne biyo bayan zaben da aka gudanar a Kano ranar Lahadi kuma ana sa ran zai kammala wa’adin mulkin tsohon shugaban kungiyar da zai kare a watan Maris na shekarar 2021.

Labbo ya ci alwashin ciyyar da kungiyar gaba musamman ta fannin tabbatar da yancin cin gashin kai na kananan hukumomi.