An yi sulhu da yan bindiga a jihar Zamfara


Kwamandodin yan bindigar dake kai hare-hare a karamar hukumar Birnin Magaji ta jihar Zamfara, a ranar Juma’a sun amince su dakatar da kai hare-hare kan mutane a wani taron zaman sulhu da ya gudana da jami’an gwamnatin jihar da kuma hukumomin tsaro.Yan bindigar sunce yanzu hanya a bude take ga mutanen da hare-haren suka shafa da su dawo garuruwansu.Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa an cimma yarjejeniyar ne a fadar Sarkin Birnin Magaji.Cikin wadanda suka halarci wurin taron akwai kwamishinan yan sandan jihar,kwamandodin yan bindigar, shugabannin Fulani, yan bijilante da kuma yan sakai.Usman Nagogo, kwamishinan yan sandan jihar shine ya jagoranci taron da ya samu halartar mai bawa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Abubakar Dauran da kuma shugabannin kungiyar Miyetti Allah.Kwamandodin yan bindigar da suka halarci taron sulhun sun hada da Ardo Nashawari,Audu Karki da kuma Muhammad Bello .Da yake magana a madadin kwamandodin,Nashawari ya ce tunda an dakatar da hare-hare yanzu manoma za su iya komawa gonakinsu sauran jama’ar gari kuma su cigaba da da gudanar da al’amuran su.Nashawari ya kara da cewa “Mun yarda da wannan tattaunawar zaman lafiya yanzu Fulani za su iya zuwa kasuwa za su iya yawo ba tare da tsangwama ba,”.Ana sa bangaren wakilin yan kungiyar Civilian JTF, Alhaji Shuaibu Aliyu ya shawarci gwamnati da ta gaggauta karfe makamai daga hannun yan bindigar.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like