An yi ruwan sama na farko a jihar Taraba


Garuruwan Gembu da kuma Dekka dake kananan hukumomin Bali da Sardauna a jihar Taraba sun samu ruwan sama na farko a wannan shekara ranar Asabar.

Rahotanni dake fitowa daga kananan hukumomin ya nuna cewa an samu ruwa sama mai yawan gaske har na tsawon sa’o’i.

Kananan hukumomin Kurmi,Gashaka, da kuma wani bangare na Bali, Takum da Sardauna sun saba samun ruwan saman farko na shekara cikin watan Janairu zuwa Faburairu.

Duk da cewa lokacin fara shuka bai yi ba ruwan da aka samu wata alama ce ga manoma na su fara shirin tunkarar shirin fara noman bana.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like