An yi jana’izar mutane 18 da yan bindiga suka kashe a Katsina


Da safiyar ranar Laraba ne akayi jana’izar gawar mutane 18 da yanbindiga suka kashe a kauyen Yar Gamji dake karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Taron jana’izar ya gudane ne a fadar Sarkin Katsina,Alhaji Abdulmumini Kabir Usman karkashin jagorancin,Ustaz Mustapha Ahmad limamin babban masallacin juma’a na jihar Katsina kana daga bisani aka binne mamatan a makabartar Dan Takum.

Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman tare da hakimai da masu rike da saurautun gargajiya da kuma jami’an gwamnati na daga cikin daruruwan mutanen da suka halarci jana’izar.

Babban limamin da ya jagoranci sallar ya yi addu’ar Allah ya jikan mamatan da rahama ya kuma bawa iyalansu da abokai hakuri da juriyar wannan babban rashin da suka yi.

Da yake magana jim kadan bayan kammala sallar jana’izar,hakimin Batsari, Mannir Rumah ya jaddada bukatar da ake kan jami’an tsaro da su kara dage damtse wajen kiyaye rayuka da kuma dukiyar jama’a.


Like it? Share with your friends!

-6
79 shares, -6 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like