An yi jana’izar Abiola Ajimobi


An gudanar da jana’izar tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi a Ibadan.

An binne shi kamar yadda addinin musulunci ya tanada a gidansa dake rukunin gidaje na Oluyole.

Tun da farko an shirya yin jana’izar marigayin a ranar Juma’a amma sai aka fasa bayan tattaunawa a tsakanin gwamnatin jihar Lagos da ta Oyo.

Ajimobi ya mutu ne ranar 25 ga watan Yuni a wani asibiti dake Lagos sanadiyar cutar Korona.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like