An Yi Garkuwa Da Wata Dalibar Jami’ar Dustin-ma (FUDMA)


Wasu bata gari da ba san ko su waye ba, sun yi garkuwa da wata dalibar sashin nazarin ilimin binciken kudi, mai shekaru 20, da ke karatu a Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) Nana Firdausi Ahmad, bayan an sace ta daga gidan mahaifinsu da ke Bayan Makarantar Mata, a Hayin Gada Dutsin-Ma, Jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa, barayin sun shiga gidan ne da misalin karfe uku na daren ranar Lahadi inda suka dauke ta sa mahaifiyar ta Baraka.

Wani mai alaka da gidan ya bayyanawa manema labarai cewa, bayan masu garkuwar sun yi nisa da gari sai suka ajiye uwar yarinyar, suka wuce da Nana.

Ya ce, “Sun bukaci a ba su miliyan 10, inda daga baya aka zabtare zuwa miliyan biyu, amma ana kan cigaba da tattaunawa.”


Like it? Share with your friends!

1
73 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like