An yi garkuwa da mataimakawa gwamnan Taraba da kuma wasu mutane 4


Wasu ƴanbindiga sun yi garkuwa da, Mallam Hassan Mijinyawa mai magana da yawun gwamnan jihar Taraba ranar Laraba akan hanyar Bali zuwa Gembu.

Sauran wadanda aka yi garkuwar da su sun hada da wasu jami’an gwamantin jihar su haɗu dake tafiya tare da Mijinyawa da kuma wani farar fata dan kasar waje da ba a bayyana kasar sa ya fito ba.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa masu garkuwa da mutanen wadanda yawansu ya kai 10 dauke da muggan makamai sun tare hanyar da safiyar yau kafin suyi garkuwa da matafiya da dama.

Mijinyawa na kan hanyarsa ta zuwa Gembu ne domin haduwa da maigidansa wanda ya tafi can tun jiya Talata domin halartar wani taro tare da babban hafsan sojan kasan Najeriya,Tukur Yusuf Buratai a garin Gembu.

An gano cewa masu garkuwa da mutanen sun tasa keyar mutanen ya zuwa cikin daji har dan kasar wajen.

Uwargidan Mijinyawa ta bayyana cewa mai gidanta ya fice daga gida da misalin karfe 7 na safe domin halartar wani taro tare da maigidansa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like