An yi garkuwa da malamin jami’a a jihar Edo


Wasu yan bindiga da ba’asan ko su waye ba sun yi garkuwa da Gideon Okedayo farfesa a sashen lissafi na jami’ar kimiyya da fasaha ta jihar Ondo.

Jaridar The Cable ta gano cewa anyi garkuwa da shi ne akan hanyar Auchi a jihar Edo me makotaka da jihar.

Dayo Temola wani ma’aikacin jami’ar ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Yawan garkuwa da mutane a sassa daban-daban na Najeriya abu ne dake ciyawa gwamnati tuwo a kwarya da ta dauki matakai iri-iri domin shawo kan batun amma abin ya ci tira.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like