An yi garkuwa da babban jami’in dan sanda a Kaduna


Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da mataimakin kwamishinan yan sanda, Isa Rambo.

Rambo wanda shine kwamandan ofishin shiya na rundunar yan sandan Najeriya dake Suleja an yi garkuwa da shi ne lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa birnin Jos.

Jaridar Punch ta rawaito cewa an yi garkuwa da babban dan sandan ranar Asabar da yamma.

“An yi garkuwa da shi a wajejen Kaduna akan hanyarsa ta zuwa Jos tare da direbansa lokacin da aka kai musu hari aka kuma yi awon gaba da su,” a cewar wata majiya da ta gana da jaridar majiyar ta kara da cewa tuni masu garkuwar suka tuntubi yan sanda inda suka bukaci kudin fansa miliyan ₦ 50.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like