An yi artabu tsakanin sojoji da mayakan Boko Haram a Damaturu


Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun samu nasarar dakile wani yunkurin kai hari da mayakan Boko Haram suka yi kan garin Damaturu babban birnin jihar Yobe.

Rundunar ta bayyana haka ne cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter dake dauke da hotunan nasarar da dakarun suka yi.

Mayakan na Boko Haram sun yi kokarin shiga garin na Damaturu ta hanyar Kukareta sai dai sun gamu da gamonsu a kwanton baunar da dakarun soja suka yi musu.

Hotunan sun nuna motocin mayakan dake dauke da bindigogin kakkabo jiragen sama wadanda dakarun suka lalata.

Harin na jihar Yobe na zuwa ne kasa da mako guda bayan da shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi ikirarin cewa an kawo karshen kungiyar ta Boko Haram.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like