An tura wani mutum gidan yari bisa zargin sace wata yarinya da yi mata fyade


Wata kotun majistire dake zamanta a jihar Kano a ranar Laraba ta tura wani mutum mai suna, Ibrahim Muntari dan shekara 38 ya zuwa gidan yari bisa zarginsa da ake da sacewa tare da yiwa wata yarinya yar shekara 15 fyade.

Muntari wanda yake zaune a Unguwar Rimin Kebe dake birnin Kano na fuskantar tuhume-tuhume biyu da suka hada da sacewa da kuma fyade.

Jami’in ɗansanda mai gabatar da kara, Insifecta Pogu Lale ya fadawa kotun cewa wata mata ce mai suna Aisha Muhammad dake zaune a unguwar ta kai karar faruwar lamarin caji ofis din ƴansanda dake Zango ranar 25 ga watan Yuni.

Lale ya ce ranar 24 ga watan Janairu mutumin da ake kara ya sace tare da kulle mai korafi yar shekara 15 a dakin abokinsa dake Rimin Kebe.

Mai gabatar da karar ya ce Muntari da kuma abokinsa wanda ya tsere sun yi lalata da yarinyar daya bayan daya har tsawon kwana guda.

Sai dai wanda ake kara ya musalta tuhumar da ake masa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like