An Tsinci Gawar ‘Yar Tsohon Mataimakin Gwamnan Ondo A Dakin Saurayinta


An tsinci gawar Oluboyo Lasisi Olugbenga a dakin saurayinta a Akure fadar jihar Ondo.

Oluboyo wacce take shekarar karshe a jami’ar Adekunle Ajasin, ta mutu ne a gidan saurayinta mai suna Adeyemi Alao, wanda aka fi sani da Q.S a safiyar ranar Lahadi.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ondo Mista Femi Joseph, ya shaidawa kanfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) aukuwar lamarin.

Femi Joseph, ya ce “babu kokonto akan faruwar lamarin saidai mutuwar matashiyar abin bakinciki ne. Ya kara da cewa muna iya kokarin mu don ganin mun samu hujjar aukuwar lamarin sannan nan da sa’oi 48 kwamishinan ‘yan sandar jihar zai yi wa manema labarai karin haske dangane da aukuwar lamarin”.


Like it? Share with your friends!

-2
113 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like