
Majalisar dokokin jihar Imo, ta tsige shugabanta,Collins Chiji daga kan kujerarsa ta shugabancin majalisar a ranar Juma’a.
An cire shi ne yayin wani zaman majalisar na musamman karkashin jagorancin mataimakinsa, Amarachi Iwuanyanwu.
Mr. Paul Emeziem mai wakiltar mazabar Onuimo shine aka zaba a matsayin sabon kakakin majalisar.
Yan majalisar sun zargin tsohon kakakin nasu da laifin rashin iya gudanar da aiki, alamundahanar kudade da kuma wasu laifuka.
Comments 144