An tsige mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Taraba


An tsige Muhammad Gwampo mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Taraba daga kan mukaminsa.

Gwampo wanda ke wakiltar mazabar Yorro an sauke shi daga kan mukaminsa ne ya yin zaman majalisar na ranar Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa an tsige shi ne kan rashin kwarewa wajen iya gudanar da aikinsa.

Tsohon shugaban masu rinjaye a a majalisar kuma mamba mai wakiltar mazabar Lau, Albasu Kunini shine ya gabatar da kudurin neman tsige mataimakin shugaban majalisar.

Bayan tsigewar an zabi mamba mai wakiltar mazabar Karin Lamido, Charles Maijankai a matsayin sabon mataimakin shugaban majalisar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like