An tsawaita dokar hana fita a Jalingo


Gwamnan jihar Taraba,Darius Ishaku ya tsawaita wa’adin dokar hana fita ya zuwa sa’o’i 24 da ya saka a babban birnin jihar Jalingo.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da, Bala Dan Abu, babban mai taimakawa gwamnan kan harkokin yada labarai ya fitar ranar Litinin a Jalingo.

Gwamnan ya umarci dukkanin hukumomin tsaro dake jihar da su tabbatar da cewa al’umma sun bi dokar sau da kafa.

A cewar sanarwar dokar hana fitar na nan daram har sai abin da hali yayi.

Kamfanin Dillanci labarai na Najeriya ya rawaito cewa an shiga murna da sowa bayan da aka sanar da Ishaku a matsayin wanda ya lashe zaben.kafin daga bisani bikin murnar ya rikide zuwa rikici da har ya kai ga asarar rayuka da lalata dukiya mai tarin yawa.


Like it? Share with your friends!

-1
55 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like