AN TAFKA MUMMUNAN MAGUDI A ZABEN KANO – Tarayyar Turai


A rahotannin da kungiyar tarayyar turai ta EU ta fitar, ta bayyana cewa a gaban jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da hukumomin tsaro aka hana masu jefa kuri’a na jam’iyyar adawa jefa kuri’unsu, a lokacin da ake gabatar da zaben gwamna na karo na biyu a jihar Kano.

Kungiyar ta kuma sanar da cewa jami’anta wadanda suka sanya ido a lokacin zaben sun yadda cewa wasu manyan jami’an gwamnatin jihar ciki hadda kwamishinoni da kuma mataimakin gwamnan jihar sun jagoranci bata sakamakon zabe, sannan kuma sun hana ‘yan jam’iyyar adawa gabatar da zabe.

Rahotannin sun bayyana cewa tasirin gwamnan na yanzu mai ci ya saka masu jefa kuri’u cikin wani hali, inda suka dinga shakkar fita wurin jefa kuri’un su, kuma hakan shine ya basu damar murde zaben, inda suka samu hadin kan jami’an gwamnati, hukumomin tsaro da kuma jami’an hukumar zabe na kasa mai zaman kanta.


Like it? Share with your friends!

-1
75 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like