An tabbatar da samun bullar cutar zazzaɓin Lassa a Adamawa


Likitoci bakwai da wasu ma’aikatan jiya biyar aka killace a Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya dake Yola jihar Adamawa bayan da suka yi mu’amala da wata mara lafiya da aka samu tana dauke da cutar zazzaɓin Lassa.

Wata majiya dake asibitin ta fadawa jaridar The Cable cewa wata mata mai juna biyu da ta rasa jaririn dake cikinta ita ce ta kamu da cutar.

Majiyar ta ce matar da aka saka a dakin yan haihuwa a ranar Juma’a an yi mata aiki inda aka cire jaririn.

Bayan cire jaririn ne sai aka lura tana zazzaɓi da zubar jini hakan yasa likitocin suka yi tunanin cewa tana dauke da cutar Lassa inda aka kebeta a wani daki na daban.

Daga nan ne aka tura jininta domin yin gwajin kwayar cutar inda aka samu sakamakon gwajin a jiya kwana biyu bayan mutuwar ta.

Ana sa ran za a cigaba da sanya idanu kan mutanen da aka ware har tsawon kwanaki 21.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like