An shawarci gwamnatin tarayya ta saka dokar ta ɓaci a jihar Zamfara


Babban limamin masallacin juma’a na Alfurqan dake Kano,Dr. Bashir Aliyu Umar ya shawarci gwamnatin tarayya da ta saka dokar ta baci a jihar Zamfara domin shawo kan yawan yin garkuwa da mutane da kuma kashe-kashen mutane da basuji basu gani ba.

Ya yi wannan kiran ne a hudubarsa ta ta sallar Juma’a da aka gabatar a masallacin.

Umar ya ce kiran ya zama wajibi domin kawo karshen kashe-kashen dake cigaba da faruwa a jihar.

“Za iya kawo karshen kashe-kashen da ake yi da kuma yin garkuwa da mutane ta hanyar samar da dokar ta ɓaci daga gwamnatin tarayya,”

Limamin yace mutanen jihar Zamfara sun cancanci a tausaya musu kan halin da suka samu kansu na kisan kiyashi da ake musu.


Like it? Share with your friends!

-1
85 shares, -1 points

Comments 3

Your email address will not be published.

You may also like