An samu nasarar ceto mutane da dama daga baraguzan ginin benen da ya ruguzo a Jos


Wani ginin bene mai hawa uku ya ruguzo inda ya jawo asarar rayukan mutane da dama a Jos babban birnin jihar Plateau.

Ginin dake unguwar Dilimi a karamar hukumar Jos ta arewa na ɗauke da shagon sayar da magani da kuma gidan wanka da bahaya.

Akalla mutane shida aka samu nasarar cetowa daga ginin inda aka kai su asibitin koyarwa na jami’ar Bingham dake Jos domin samun kulawa.

Jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA da kuma na hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Plataeu sune suka jagoranci ayyukan ceto mutanen da abun ya rutsa da su.

Kefasa Yilrwang shugaban hukumar dake lura da birnin Jos ya ce rashin kayan ya taimaka matuka wajen kawo tsaiko a yayin da suke gudanar da aikin ceto.


Like it? Share with your friends!

1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like