An samu mutum na uku da ya kamu da Coronavirus a Bauchi


Gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da samun mutum na uku dake dauke da cutar Coronavirus a jihar.

Mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban kwamitin yaki da cutar a jihar,Baba Tela shine ya bayyana haka ranar Talata a asibitin Bayara dake Bauchi lokacin da yake wa manema labarai jawabi kan bullar cutar a jihar Bauchi.

Ya ce cikin samfuri 23 da aka aike da shi hukumar NCDC mai yaki da cututtuka masu yaduwa an tabbatar da samun mutum guda dan shekara 56 na dauke da cutar Coronavirus.

Ya ce tuni aka killace marar lafiyar inda aka fara yi masa magani ba tare da bata lokaci ba.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like