An samu karin mutane 664 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya


Adadin yawan masu cutar Korona a Najeriya ya samu karuwa sosai a ranar Asabar bayan da aka tabbatar da mutane 664 na dauke da cutar cikin jihohi 17 da kuma birnin tarayya Abuja.

Hukumar NCDC dake yaki da cututtuka a Najeriya ita ce ta sanar da haka cikin wani sako da ta wallafa da misalin karfe 11:46 na ranar Asabar.

Idan aka dauke jihar Lagos da ta samu karin mutane 224 birnin tarayya Abuja shi ne na biyu da yawan mutane 105 sai kuma jihar Edo dake da mutane 85 inda suka kasance kan gaba a yawan mutane.

Har ila yau yawan wadanda suke warkewa daga cutar ya karu matuka inda aka samu mutane 308 da suka warke.

Amma kuma an samu mutane 15 da suka mutu a sanadiyar cutar ta Korona cikin sa’o’i 24.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like