An samu karin mutane 136 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya


Hukumar NCDC dake dakile cututtuka masu yaduwa a Najeriya ta sanar da samun Karin mutane 136 da suka kamu da cutar Korona a fadin kasa baki daya

Bayanin karin mutanen da suka kamu da cutar na kunshe ne cikin sanarwar da hukumar ta saba fitarwa a ko wace rana kan halin da ake ciki a yaki da ake da cutar a fadin Najeriya.

Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa jihar Lagos na kan gaba da yawan mutanen da suka kamu da cutar inda aka samu karin mutane 41 sai kuma jihar Ogun dake biye mata baya da mutane 27.

Kawo yanzu dai jumullar mutane 58,198 ne suka kamu da cutar ayayin da mutane 49,722 suka warke sumul daga cutar.

Cikin wannan adadi mutane 1,106 ne suka mutu.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 1

You may also like