An samu fitowar masu zaɓe da yawa a garin Kankia a zaɓen cike gurbin da ake a Katsina


An samu fitowar mutane masu yawa a zaben cike gurbin dan majalisar dattawa na mazabar arewacin Katsina da ake gudanarwa yau Asabar.

Fitattun yan takara biyu a zaben, Ahmad Babba Kaita na jam’iyar APC da kuma Alhaji Kabir Babba Kaita na jam’iyar PDP sun fito ne daga gida daya.

Wakilin jaridar Daily Trust ya lura cewa an samu fitowar jama’a masu yawa a tashoshin zabe daban-daban dake garin.

Da yake magana da manema labarai, tsohon dantakarar kujerar gwamnan jihar karkashin jam’iyar PDP a zaben shekarar 2015, Alhaji Musa Nashuni ya yabawa jami’an ƴansanda da kuma hukumar zabe kan yadda ake gudanar da zaben lami lafiya.

“Na ji dadi zaben yana gudana cikin lumana.tabbas wannan zaɓen cike gurbin zai bawa yan Najeriya kyakkyawan fata cewa za a gudanar da zaɓen shekarar 2019 lafiya,” ya ce.


Like it? Share with your friends!

2
105 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like