An sako yan agaji 20 da akayi garkuwa da su


Ƙungiyar JIBWIS ta tabbatar da sakin jami’an agajinta su 20 da akayi garkuwa da su ranar 23 ga watan Disamba a karamar hukumar Jibia dake jihar Katsina.

Shugaban majalisar malaman kungiyar Sheikh Sani Yahaya Jingir shine ya sanar da sakin yan agajin a wani taron manema labarai a Jos.

Ƙungiyar ta JIBWIS ta bayyana cewa an saki mutanen ne da misalin karfe daya na dare a garin Dauran dake karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Idan za a iya ranar 31 ga watan Disamba ne kungiyar ta sanar da sace ƴaƴanta su 20 a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina lokacin da suke kan hanyar komawa gida Sokoto bayan da suka halarci taron horo na yan agaji da aka gudanar a Dutse babban birnin jihar Jigawa.


Like it? Share with your friends!

-1
62 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like