Rahotanni daga jihar Nejan Najeriya na nuna cewa an sako Kwamishinan labarai na Jihar Alh. Sani Idris da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi.

A ranar Lahadin da ta gabata, ‘yan bindigar suka sace Idris a yankin Baban Tunga da ke karamar hukumar Tarfa.

Ko da yake, dai Gwamnatin jihar Nejan ta ce ba ta da masaniya akan tabbacin sako kwamishinan, amma mataimaki na musamman ga kwamishinan Malam Iliya Garba ya ba da tabbacin cewa an sako kwamishinan.

A cewar Garba an sako shi ne bisa kokarin iyalansa ba tare da biyan kudin fansa ba.

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja)

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja)

“Muna godiya ga Allah da ya dawo mana da shi da ransa, iyalansa suka dauke nauyin komai da komai da rokon Allah, Allah kuma ya amsa addu’a.” In ji Garba.

A lokacin da na tuntubi sakataren Gwamnatin jihar Nejan Alh. Ahmed Ibrahim Matane ya ce ba su da labarin tabbacin sako kwamishinan domin ba su yi magana da iyalansa ba.

Har ya zuwa yanzu dai daliban Islamiyyar Salihu Tanko sama da dari na hannun ‘yan bindigar a jihar kimanin makonni goma kenan duk kuwa da kudi sama da naira Miliyan 50 da iyayen yaran suka biya a matsayin kudin Fansa.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari: