An saki Orji Kalu daga gidan yari


An saki tsohon gwamnan jihar Abia,Orji Uzo Kalu daga gidan yari.

Aka Kalu, lauyan dake jagorantar lauyoyinsa, shi ne ya tabbatarwa d jaridar The Cable sakin nasa.

Hukumar EFCC dake yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ita ta gurfanar da Kalu da Ude Jones tsohon daraktan kudi a jihar Abia a gaban kotu inda ake musu tuhume-tuhume 36 da suka shafi almundahanar kudade da yawansu ya kai biliyan ₦7.2 aka kuma daure su a cikin watan Disamba.

A ranar 8 ga watan Mayu ne kotun koli ta soke baki dayan shari’ar da aka yi wa mutumin da ake tuhumarsa tare da Kalu.

Hakan yasa lauyoyin Kalu suka garzaya gaban kotun inda a ranar Talata wata babbar kotun tarayya dake Lagos ta bayar da umarnin a saki shi.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like