An sake samun wani gini ya ruguzo kan wasu magidanta a Lagos


Wasu mazauna wani gida dake yankin Oke Arin a jihar Lagos na can sun makale cikin baraguzai bayan da ginin gidan da suke ciki ya rufta.

Wani mazaunin yankin ya shedawa jaridar The Cable cewa lamarin yafaru ne da misalin karfe uku da minti arba’in da biyar na yammacin ranar Litinin.

A jiya ne gwamnatin jihar Lagos ta fara rushe wasu gidaje da suka nuna alamar rugujewa a kokarin da gwamnatin keyin na kaucewa makamancin abin da ya faru a yankin Ita Faji dake jihar inda wani ginin bene mai hawa uku dake ɗauke da makarantar firamare ya ruguzo inda aka samu asarar rayuka da dama.

Gwamnatin jihar ta gargadi mutanen dake cikin gidajen da aka yiwa alamar za a rushe su.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like