An sake nuno gwamna Ganduje yana likimo wajen taron da ya raka Buhari kasar Afrika ta Kudu


Wani sabon hoto na gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yadu a shafukan sada zumunta, inda aka nuno shi yana bacci hadda minshari a wajen wani taro da suka halarta shi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kasar Afrika ta Kudu.

Gwamna Ganduje dai yayi wan nan tafiyar ne da shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar Larabar nan, wata ziyara da shugaban kasar ya kai kasar Afrika ta Kudu, domin bin kadi akan kisan ‘yan Najeriya da ake yi a kasar Afrika ta Kudu.

A lokacin ziyarar, gwamnatin Najeriya ta hadu da gwamnatin kasar Afrika ta Kudu domin su samo masalaha dangane da kashe ‘yan Najeriya da ake yi a kasar ta Afrika ta Kudu.

A yayin da ake gabatar da wannan taron ne aka hango gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje yana sharar bacci hadda minshari.

Idan ba a manta ba makonnin da suka gabata ne ‘yan kasar Afrika ta Kudu suka dinga bi suna kashe baki mazauna can suna bankawa shagunansu wuta bayan sun debe kayan ciki.

Wannan dalili ne ya sanya gwamnatin Najeriya ta nemi duka ‘yan Najeriya mazauna can da su dawo gida Najeriya.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like