An sake kama wasu daga cikin fursunonin da suka tsere a Benin


Rundunar yan sandan jihar Edo ta sake kama wasu daga cikin daurarrun da suka tsere daga gidajen yarin da aka balle a yayin zanga-zangar EndSARS a jihar.

Shida daga cikin wadanda suka tsere an kama su ne da laifin aikata fashi da makami a yayin da aka kama mutum daya lokacin da yake kokarin kisan mutumin da ya bada sheda akan sa a gaban kotu.

Daurarrun su goma na daga cikin mutane 120 da rundunar ta kama da ake zargi da hannu a fasawa tare da daka wawa na kayan abinci da ma wasu kayayyaki a ofishin hukumar kwastam da kuma wasu rumbunan ajiye kayayyakin abinci na wasu kamfanoni dake jihar.

Kwamishinan yan sandan jihar,Johson Kokuman ya bayyana sunan daurarrun da aka sake kamawa da suka hada da Emmanuel Udoh, Friday Etim, Victor Akpotor, Lucky Precious, Osarumen Enoragbon, Patrick Eguavoen, Abraham Matthew, Endurance Ifobuow, Mohammed Adamu da Henry Atadi.

Ya ce Henry Atadi bayan tserewarsa daga gidan yarin ya samu nasarar kwace wata mota kirar Lexus inda aka kama shi da ita a Okada.


Like it? Share with your friends!

1

Comments 10

Your email address will not be published.

You may also like