An sake harbe wani ɗan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu


Wani ɗan bindiga ya kashe, Ozumba Tochukwu Lawrence wani dan Najeriya dake zaune a kasar Afirka ta Kudu.

David Abraham, mai magana da yawun babban jakadan Najeriya a kasar ta Afirka ta kudu shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Abraham ya ce jakadan cikin yanayin ciwo da alhini ya samu labarin kisan Tochukwu-Lawrence.

Ya ce mummunan lamarin yafaru ne ranar Juma’a, a Mpumulanga dake kasar ta Afrika ta Kudu.

Sanarwar ta e “wani da ya sheda abin da ya faru ya bayyana cewa wani mutum da ba a san waye shi ba ya shiga harabar gidan Mista Ozumba Tochukwu-Lawrence inda ya nemi ya gana da shi.

“Bayan da aka fada masa yana da bako, ya fito domin ya gana da shi sai mutumin ya bude masa wuta inda ya harbe shi har sau shida hakan ya jawo mutuwarsa kafin a karasa da shi asibiti.

“Har yanzu ba a iya gano dalilin da yasa aka aikata wannan abu mara daɗi ba amma abune da bai daceba kuma ya kamata ayi allawadai da shi.”

Sanarwar ta ci-gaba da cewa Ofishin zai cigaba da aiki da jami’an tsaron kasar domin gano wadanda ke da hannu a kisan.

Kashe yan Najeriya ba sabon labarin bane a kasar Afirka ta Kudu abune dake nema ya zama ruwan dare.

Sai dai a lokuta da dama hukumomi na bada tabbacin bincike, ganowa da kuma gurfanar da masu aikata irin haka a gaban kotu.


Like it? Share with your friends!

2
91 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like