An Saka Dokar Takaita Zirga-zirga A Birnin Aba Na Jihar Abia 


Gwamna Okezie Ikpeazu,na jihar Abia ya saka dokar takaita zirga-zirga  a garin kasuwanci na Aba dake jihar biyo bayan tashin hankalin da aka samu.

Yayan kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra wacce Nmandi Kanu ke jagoranta yanzu haka na zaman doya da manja da sojojin Najeriya.

Dokar takaita zirga-zirga zata fara ne daga karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00na safe daga yau Talata har zuwa ranar Alhamis. 

A wata sanarwa da yafitar yau Talata Ikpeazu ya bayyana damuwarsa kan yadda sojoji suke gudanar da aikinsu a garin.

Amma kuma yace gwamnati zata hada kai da hukumomin tsaro wajen dawo da doka da oda. 

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like