An sace yan sanda biyu a Rivers


Yan bindiga sun sace wasu yan sanda biyu Ngo dake karamar hukumar Andani ta jihar Cross River.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN an sace jami’an yan sandan ne ranar Litinin.

Ya zuwa lokacin da aka wallafa wannana rahoton bayanai ba su gama bayyana ba kan faruwar lamarin.

Mai magana da yawun yan sandan jihar,Nnamdi Omoni ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai ya gaza yin cikakken bayanin abin da ya faru.

Tabarbarewar sha’anin tsaro a jihar abu ne da ya damu gwamnatin jihar

A ranar Lahadi ne wasu yan bindiga suka dauki tsawon lokaci suna musayar wuta da yan bindiga a karamar hukumar Khana ta jihar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like