An sace dalibai mata 6 da malamai biyu daga wata makaranta a Kaduna


Akalla dalibai mata 6 da malamai biyu aka sace a kwalejin Engraver dake Kakau Daji a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Daya daga cikin iyayen daliban da aka sace ya fadawa jaridar The Cable cewa ya amsa kiran waya daga masu garkuwar ranar Alhamis da safe.

“Sun fadawa yata ta basu nambar da za su kirawo shi ne lokacin da suka kirawo ni.Amma kuma na kasa fahimtar ko suna tambayar kudin fansa ne saboda suna magana ne da yaren da bana ji,” ya ce.

“Nayi magana da ‘yata daga nan suka kwace wayar daga hannunta suka katse kiran.”

Yakubu Sabo mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya tabbatar da sace daliban inda ya ce yan bindigar sun shiga makarantar ne ta wurin da babu katanga.

Ya ce suna shiga makarantar sun wuce kai tsaye dakin kwanan dalibai mata inda suka sace su.

Ita ma gwamnatin jihar Kaduna ta bakin kwamishinan tsaron cikin gida na jihar,Samuel Aruwan ya tabbatarwa da BBC Hausa faruwar lamarin.


Like it? Share with your friends!

-1
83 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like