An rusa gidan da ake garkuwa da mutane a ciki a Kano


Ma’aikata daga hukumar tsara birane ta jihar Kano KNUPDA bisa rakiyar jami’an tsaro sun rushe gidan da aka samu wasu masu garkuwa da mutane a ciki.

Hakan ya biyo kama wata mata da rundunar yan sandan jihar tayi wacce take haya a gidan kuma take yin garkuwa da mutane a ciki.

Matar mai suna Maryam Muhammad da ake kira Hajiya ta kama hayar gidan ne a unguwar Jaba dake karamar hukumar Ungoggo ta jihar inda suke aikata laifin da taimakon wasu maza su huɗu.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 25

You may also like