A wani taron manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwar jihar, kwamishinar kula da harkokin ilimin jihar Hajiya Hannatu Jibiril Salihu ta ce daga cikin makarantun kwana guda 56 dake sassan jihar guda 25 kacal ke bude suna aiki a halin yanzu.

Wannan dai yana zuwa ne a daidai lkacin da aka samu canjin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Alhaji Adamu Usman a sakamakon karin girman da ya samu.

Amma kuma kwamishinan kananan hukumomin jihar Nejan Barrista Abdul-Malik Sarkin Daji ya ce suna fatar samun jajirtaccen sabon shugaban ‘yan sandan bayan la’akkari da yadda jihar Nejan ke fama da matsalar kalubale irin na tsaro.

A halin da ake ciki dai har yanzu daliban Islamiyyar Salihu a jihar Nejan na hannun ‘yan fashin daji sama da watanni biyu kenan duk kuwa da Naira miliyan 30 da iyayen yaran suka ce sun kai ma ‘yan fashin a matsayin kudin fansar yaran.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: