An rufe majalisar dokokin Anambra bayan wasu yan majalisar sun kamu da cutar Korona


An rufe ginin zauren majalisar dokokin jihar Anambra har na tsawon makonni uku bayan da wasu yan majalisar suka kamu da cutar Covid-19.

A ranar 19 ga watan Janairu ne majalisar ta gayyaci kwamitin yaki da cutar Korona na jihar domin gudanar da gwajin kwayar cutar ga dukkanin mambobinta da kuma ma’aikatanta.

A yan kwanakin nan an samu karuwar yawan mutanen da suke fama da cutar a jihar abin da yasa majalisar ta ce dole sai an yi kowanne dan majalisar gwajin.

Sakamakon gwajin da aka gudanar ya nuna cewa wasu daga cikin yan majalisar na dauke da cutar ta Korona.

A yayin wani zaman gaggawa ranar Laraba shugaban majalisar, Uche Okafor ya sanar da dage zaman majalisar.

Shugaban ya ce za a yi feshin magani a a majalisar da kuma gidajen wadanda aka samu sun kamu da cutar.

Babu bayani kan yawan yan majalisar da suka kamu da cutar.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 1

You may also like