An rufe hanyar Mokwa zuwa Jebba bayan ruwan sama ya rushe wata gada


Wata gada dake kan hanyar Mokwa zuwa Jebba ta rushe da safiyar yau Lahadi bayan wani mamakon ruwan sama.

Rushewar gadar ya janyo tsayawar zirga-zirgar ababen hawa a kowane bangare na titin.

Bisi Kazeem, mai magana da yawun hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa, FRSC shine ya ankarar da jama’a faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Ya ce gadar dake da nisan kilomita 18 daga garin Mokwa na jihar Niger ta rufta ciki bayan mamakon ruwan sama.

“Lamarin ya shafi zirga-zirgar ababen hawa ta kowanne bangare,” Kazeem ya ce.

“Ana shawartar masu motoci da su bi hanyar Lokoja idan za su je Lagos ko a Abuja a matakin wucin gadi.”

Hanyar Mokwa zuwa Jebba wata babbar hanya ce ga matafiya tsakanin Abuja da Ilorin.

Kazeem ya ce wurin da lamarin ya faru bai wuce tazarar kilomita guda ba daga Gadar Tatabu wacce ta ruguje a shekarar da ta wuce.

Ya ce tuni hukumar ta kara tura karin jami’anta zuwa yankin domin tabbatar da cewa an samu cigaba da zirga-zirga ba tare da matsala ba.


Like it? Share with your friends!

2
84 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like