An rantsar da Oyetola a matsayin sabon gwamnan jihar Osun


Da karfe 12:30 na rana aka rantsar da Gboyega Oyetola a matsayin sabon gwamnan jihar Osun.

Oyetola wanda ya lashe zabe karkashin jam’iyar APC, an rantsar da shi a filin wasa dake garin Osogbo.

Cikin wadanda suka halarci bikin rantsuwar sun hada da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Maigida Mustapha wanda ya wakilci shugaban kasa,Muhammad Buhari; Adams Oshimhole shugaban jam’iyar APC na kasa da kuma Bola Ahmad Tinubu jagoran jam’iyar APC na kasa.

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredelu,Abiola Ajimobi na jihar Oyo, Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, da kuma Akinwumi Ambode na jihar Lagos na daga cikin gwamnonin da suka halarci wurin taron.

Oyetola ya kasance gwamnan jihar na mulkin farar hula na biyar tun bayan da aka kirkiri jihar a shekarar 1991.


Like it? Share with your friends!

1
93 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like