An rantsar da Onoja a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kogi


An rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar Kogi.

Onoja shine ke yiwa gwamnan jihar, Yahaya Bello takarar mataimaki a zaben gwamna da za a gudanar ranar 16 ga watan Nuwamba me zuwa.

Babban alkalin alkalai na jihar,Nasir Ajanah shine ya jagoranci bikin rantsuwar da ya gudana a gidan gwamnati dake Lokoja.

Bikin ya gudana ne biyo bayan tabbatar da shi da majalisar dokokin jihar ta yi.

Gwamna Yahaya Bello ya mika sunan Onoja ga majalisar dokokin jihar a matsayin wanda zai maye gurbin, Simon Achuba tsohon mataimakin gwamnan jihar.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like