An rantsar da Fayemi a matsayin gwamnan Ekiti


Mutumin da ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti da aka gudanar ranar 14 ga watan Yuli, 2018, Kayode Fayemi da kuma mataimakin sa, Cif Adebisi Egbeyemi, sun karbi rantsuwar kama aiki daga bakin babban jojin jihar, mai shari’a Ayodeji Daramola.

Da Karbar rantsuwar kama aikin yanzu sun zama gwamna da kuma mataimaki.

Bikin rantsuwar ya gudana a wurin taro na Ekiti Parapo Pavillion dake Ado Ekiti babban birnin jihar.

Bikin ya samu halartar jiga-jigan jam’iyar APC ciki har da jagoran jam’iyar na kasa Bola Ahmad Tinubu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like