An Rage Harajin Da Aka Sakawa Kayayyakin Da Ake Shigo Da Su Nijeriya, Kwanan Nan Motoci Za Su Yi Arha, Cewar Shugaban Kwastam


Shugaban hukumar yaki da masu fasa-kauri a Nijeriya Hameed Ali, ya shaida wa ‘yan jarida a birnin tarayya Abuja cewa suna jiran umarni daga gwamnati a halin yanzu.

Kanal Hameed Ali (mai ritaya) ya bayyana cewa kowane lokaci daga yanzu (a jiya), takarda za ta iya fito wa daga ofishin Ministar tattalin arziki na kasa.

Jaridar Punch tace ana sa ran cewa a makon gobe ne ragin kudin harajin da gwamnatin tarayya ta yi wajen shigo da motoci daga kasar waje zai fara aiki.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like