An nemi Buhari ya shiga tsakanin rikicin majalisar dokokin jihar Akwa Ibom


Gwamnan jihar Akwa Ibom,Udom Emmanuel ya yi kira ga shugaban kasa,Muhammad Buhari da ya shiga tsakani a rikicin dake faruwa a majalisar dokokin jihar domin tabbatar da cigaba da samun tsaro a jihar.

Emmanuel ya fadi haka a wani taron manema labarai da ya gudanar a masaukin gwamna dake Uyo ranar Talata bayan yamutsin da ya faru a majalisar dokokin jihar.

Ya ce jihar za ta cigaba da zama lafiya duk da kawanyar da jami’an tsaro suka yiwa ginin majalisar dokokin jihar.

“Muna kira ga shugaban kasar tarayyar Nigeria, Muhammadu Buhari domin muma yan kasa ne kuma yakamata shugaban kasa ya dauki matakin da ya dace domin kawo karshen abinda ke faruwa lallai munga alamun haka.

“Inaso na yarda cewa mutane na za su samu kariya daga kundin tsarin mulki da kuma dokokin kasarnan.”

Gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka jibge jami’an ƴansanda a harabar majalisar dokokin jihar kana ya yi kira da a ɗauke kwamishinan ƴansandan jihar,Musa Kimo daga jihar.


Like it? Share with your friends!

-1
91 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like